Harin Jirgin Abuja: Gumi Ya Shawarci Gwamnati Ta Biya ‘Yan Bindiga Fansa

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar shahararren malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta jihar ta biya ‘yan ta’adda kudin fansa don ceto fasinjojin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna su 62 da aka yi garkuwa da su.

Malamin ya bayyana haka ne a yayin addu’o’i na musamman da Jam’iyyar Matan Arewa ta shirya don wadanda ake garkuwa da su, wanda ya gudana a garin Kaduna.

A ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasa dauke da fasinjoji  da ke kan hanyarsa ta zuwa kaduna daga Abuja, inda suka kashe wasu tare da awon gaba da adadi mai yawa na Fasinjoji.

Gumi ya ce ‘yan siyasa na daukar kudi har sama da Naira miliyan 50 don sayen tikitin takara, a maimakon biyan kudin fansa don ceto wadanda ake garkuwa da su.

Labarai Makamanta