Harin Jangeɓe: Akwai Mata Cikin ‘Yan Bindigar Da Suka Kai Hari

Wasu daga cikin Daliban Sakandiren Jangebe da suka tsallake rijiya da baya, sun ce har da mata a cikin gungun ’yan bindigar da suka kai hari makarantar a daren Juma’a.

Wata daga cikinsu mai suna Madina Hamisu Kawaye, ta ce tana tsaka da sharar bacci wata mata rike da bindiga ta tashe ta.

“Ina cikin bacci wata mata sanya da bakaken kaya ta farkar dani ta hanyar buga bindigarta a jikin gadajen da muke kwance.”

“Na farka a gigice, sai na lura dukkanin ’yan dakin namu an kora su waje kuma wasunsu sun lullube jikinsu da bargo.”

Madina ta ce “sai na sulale na buya a karkashin wani gado inda na riski wasu daliban biyu suma sun buya yayin da matar ta tafi tashin sauran daliban da ba su farka ba.”

“Na jiyo wani daga cikin ’yan bindigar yana magana ta wayar salula, yana labarta cewa sun shiga makarantar kuma sun fara tattara dalibai.”

Ta ce daya daga cikin ’yan bindigar ya yi magana da Fulatanci.
Haka kuma wata dalibar da ita ma ta tsira mai suna Zainab, ta ce wani bandaki ta samu ta buya a yayin da maharan ke tattara daliban a kusa da masallacin makarantar.

“A cikin taron dalibai na tsinke a guje na buya a wani bandaki, inda a nan na fake har zuwa lokacin da na ji fara jin harbin bindiga da kuma motsin motoci a yayin da aka tafi da daliban a cikinsu.”

Hoto: The Cable
Wasu daga cikin fuskokin daliban da suka tsira

Labarai Makamanta