Hari Gidan Alkalin Babbar Kotu: An Gurfanar Da Wadanda Ake Zargi

An gurfanar da wasu mutane 15 gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin kutsa kai gidan mai shari’a ta kotun kolin Mary Odili a cikin watan Oktoban da ya gabata.

Ana zargin mutanen, waɗanda suka bayyana kansu a matsayin jami’an tsaro, sun kutsa kan su gidan ne, da nufin gudanar da bincike, bisa zargin ana aikata wasu abubuwa da suka saɓa doka a cikin gidan.

A cikin watan Nuwamban da ya gabata ne, rundunar ƴan sanda ta gabatar wa manema labarai, mutanen 15 da ake zargi da kutsa kai gidan mai shari’a Mary Odili.

Mutanen da runduanar ta ce, babu wata hukumar tsaro a Najeriya da ta san da su, cikinsu kuwa har da wani cif sufuritandan na ƴan sanda na bogi.

Rundunar ƴan sandan na zargin mutanen da sauran wasu bakwai da suka tsere, da haɗin baki, suka shiga gidan mai shari’a Mary Odili, wadda yanzu haka ita ce ta biyu a girman mukami a jerin alkalan kotun kolin Najeriya.

Labarai Makamanta