Harbo Jirgin Yaki: Rundunar Soji Ta Karyata Boko Haram

Rundunar Sojin saman Najeriya sun musanta iƙirarin da ƴan ƙungiyar boko haram suka yi a wani bidiyo na harbo jirgin yaƙin sojojin da aka nema aka rasa tun ranar Laraba, 31 ga watan Maris.

Kamar yadda kafafen Jaridu suka wallafa, Boko haram sun saki wani bidiyo suna tabbatar wa da duniya cewa sune suka harbo jirgin yaƙin.

Sai dai babban jami’in hulɗa da jama’a na sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya musanta maganar wannan bidiyon da ƴan Boko Haram suka saki.

Ya ƙara da tabbatar wa da duniya cewa ƴan Boko Haram sun lailayo wata ƙaryar ne kawai suka maka duk don su ƙara wa labarin armashi amma maganar gaskiya ba haka bane.

Kamar yadda kakakin NAF din, Air Commodore Edward Gibkwet yace: “Mun ga wasu bidiyoyi suna yawo wadanda babu wata alama da take nuna cewa jirgin namu ne, ko kuma wani matuƙin jirginmu ko kuma alamar jirginmu ne wannan wanda suke nunawa.

“Da alama wani bidiyo ne can daban da aka ɗauka a wani wuri wanda ko shuke-shuken wurin ba na arewa maso gabas bane. Suna ta sakin bidiyoyin da kadan-kadan kuma muna kallo.”

Labarai Makamanta