Har Yanzu Ni Ɗan Siyasa Ne – Ɗan Tsohon Shugaban Kasa Murtala


Dan tsohon Shugaban Kasa Murtala Muhammed ya musanta rahotanni da ke yawo a kafafen yada labarai cewa ya ajiye siyasa baki daya.

Abba Risqua Murtala Mohammed wanda shi ne babban dan Janar Murtala ya shaida wa BBC cewa batun ya daina siyasa wani tsohon labara ne da ya taba faruwa tun shekarar 2017, “kuma ko a wancan lokacin na ajiye siyasar ne na wani dan lokaci”.

Abba ya kara da cewa a makon da ya gabata ne ya koma jam’iyya mai mulki ta APC a jiharsa ta Kano, inda ya taba yin takarar mataimakin gwamna a 2015 karkashin jam’iyyar PDP.

A cewarsa gwamnan Kano da mutanen jihar baki daya ba su ji dadin wannan labara ba, ganin cewa bai dade da bayyana kansa a matsayin mamba na jam’iyyar ba, kuma gwamnan ya yi maraba da shi a mataki na jiha.

Labarai Makamanta