Har Yanzu Ni Ɗan PDP Ne – Fani-Kayode

Tsohon ministan sufurin jiragen Samann Najeriya, Femi Fai-Kayode ya karyat gwamnan Kogi bayan shelar da gwamnan yayi cewa Fain-Kayoden ya dawo Jam’iyyar APC.

Gwamnan Bello ya yi shelar cewa Fani-Kayode ya canja sheka bayan wani ganawa da suka yi da shi ya dawo jam’iyyar APC.

Tuni Fani-Kayode ya karyata gwama Yahaya Bello, yace gwamnan katobara yayi, shi Fani-Kayode bai fice daga PDP ba yana nan cikin ta daram dam.

Yace idan ba a shafinsa aka ga ya saka ya canja sheka ba kada a yarda da maganan wani can.

” Eh, mun dan tautauna game da makomar siyasar Najeriya, amma ni ban canja sheka ba.Ina nan a PDP daram dam.”

In dai jama’a basu manta ba a makon da ya gabata ne labarin komawa jam’iyyar APC na Fani-Kayode ya cika kafafen yada labarai a ruwayar Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, kamar haka…

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana wa dandazon magoya bayan APC a jihar Kogi cewa tsohon ministan sufurin jiragen Sama na Kasa, Femi Fani-Kayode ya dawo jam’iyyar APC.

Yahaya Bello ya bayyana cewa dama can da shi Femi aka aza tubalin kafa jam’iyyar APC kafin saɓani ya sa ya fice daga jam’iyyar ya koma wata jam’iyyar.

” Ina so in tabbatar muku yau cewa fitaccen ɗan siyasa Fani-Kayode ya dawo gida, wato APC, kuma muna maraba da shi.

Idan ba a manta ba an rika saka hotunan gwamna Yahaya da shugaban jam’iyyar APC, gwamnan Yobe, Mala Buni da Fani-Kayode a shafukan yanar gizo a lokacin da ake tartaunawa.

Fani Kayode na daga cikin wadanda suke yin tsananin adawa ga jam’ iyyar APC tun bayan kasa PDP da ta yi a zaben 2015.

Sannan kuma da nuna tsananin kiyayyarsa ga musamman yankin Arewa wand wasu ke gani bai taba fadin alkhairi ga gwamnatin Buhari da yankin Arewa ba.

Labarai Makamanta