Har Yanzu Ina Tababar Ko Buhari Ke Mulkin Kasar Nan – Soyinka

Sanannen Farfesan harshen turanci mazaunin ƙasar Amurka Farfesa Wole Soyinka, ya ƙara jaddada cewa shi fa har yanzu bai yarda Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke mulkin Najeriya ba.

Wole Soyinka ya bayyana hakan ne yayin jawabi kan matsalar tsaro a wani shiri na gidan Talabijin na Arise TV dake birnin Ikko.

Ya ce dubi ga irin abubuwan dake faruwa a fadin tarayya, baya tunanin Buhari ya san abubuwan dake faruwa tsakanin manoma da makiyaya na kazamcewar rikici da zubar da jini.

“Na dade ina fadin wannan kuma ina sake jaddadawa, Buhari bai san abubuwan dake faruwa ba. Bai fahimci halin da ake ciki ba,” Soyinka yace.

“Saboda a fahimta ta, ba zai yiwu shugaban kasa, shugaban jami’an Sojojin kasa ya ce shi ke jagoranci amma abubuwa su tabarbare haka ba, lallai akwai babban matsala cikin lamarin shugabancin kasar nan.”

Wole Soyinka ya yi fashin baki kan rahoton cewa makiyaya sun kai hari gidansa dake jihar Ogun. Ya ce kawai wasu shanu ne suka shiga gidansa kuma ya kore su.

Mun kawo muku cewa hukumar ‘yan sandan jihar Ogun ta sanar da cewa shanun da suka kutsa cikin gidan Wole Soyinka na wani bayerabe ne. A yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya ce shanun na wani Kazeem Sorinola ne wanda ya dauki wani bafulatani wanda yake kula da shanun.

“Shanun na wani bayerabe ne mai suna Kazeem Sorinola. Ya bai wa wani bafulatani kula da shanun ne. Shanun ba na bafulatanin bane, dan tsaro ne kawai,”.

Labarai Makamanta