Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta ce har yanzu matakan da ta dauka suna nan daram, na hana zirga-zirga da babura da sayar da mai a jarka a wasu kananan hukumomi dake jihar da cin kasuwannin mako mako da kuma safarar dabbobi.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Gwamna El-Rufai ya ba jama’ar jihar hakuri bisa wannan mataki wanda yace daukarsa ya zama wajibi saboda tsaron dukiya da rayukan jama’a, sai dai Aruwan ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara a dan lokacin da aka katse layukan sadarwar.
You must log in to post a comment.