Har Yanzu Ba Mu Ayyana Dan Takarar Da Za Mu Goyi Baya Ba – Dattawan Arewa

Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana dalilan da ya sa har yanzu bata bayyana zabinta cikin yan takarar kujerar shugaban kasa a zaben da zai gudana watan gobe ba.

Za’a gudanar da zaben shugaban kasan Najeriya ranar 25 ga Febrairu, 2023. Wadanda ake yiwa kallon cikinsu daya zai lashe zaben shugaban kasan sun hada Peter Obi (Labour Party), Bola Tinubu (All Progressives Congress) , Atiku Abubakar (Peoples Democratic Party) da Rabiu Kwankwaso (New Nigeria Peoples Party).

Mai magana da yawun dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce ba zasu yi gaggawan ayyana wanda zasu goyi baya ba duk da ana sauran yan makonni zabe.

“Wannan karon muna takatsantsan – bamu son yin gaggawan hukunci. Akwai saura makonni shida kan mu yanke shawara. Muna bibiyan abubuwan da yan takara ke yi, abubuwan da suka fadi, har da yan takaran gwamna da majalisa.”

Ya kara da cewa zasu sanar da wanda suke goyon baya kafin ranar zabe saboda ba zasu bari Arewa ta zauna ba tada matsaya ba.

Labarai Makamanta