Har Yanzu Akwai Sauran Dalibai A Hannun ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Kaduna

Dakarun sojojin Nijeriya sun samu nasarar ceto daliban Kwalejin Koyon Gandun Daji ta Tarayya, dake yankin karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna. ‘Yan bindigar sun far wa makarantar da misalin karfe 11:30 na ranar Alhamis kuma suka yi awon gaba da dalibai da ma’aikata.

‘Yan bindigar da ke dauke da makamai sun kutsa kai cikin makarantar ta hanyar fasa ginin dake kewaye da makarantar.

Sojojin sun yi nasarar kubutar da Daliban su 180, Dalibai mata 42, ma’aikata 8 da dalibai maza 130. Wasu daga cikin daliban da aka ceto sun ji rauni kuma a yanzu haka suna karbar kulawar likita a wani sansanin sojoji.

Sai dai a wata sanarwa da kwamishinan kula da harkokin tsaro na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar a shafin sa na Facebook, ya bayyana cewar har ya zuwa wannan lokacin da akwai sauran ɗalibai 39 a hannun ‘yan Bindigar.

Labarai Makamanta