Har Yanzu Ɗaliban Jangeɓe Na Hannun ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Zamfara

Rahotonni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Daliban da aka sace daga makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnati dake Jangebe, a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara, har yanzu suna tare da wadanda suka sace su, in ji gwamnatin jihar.

Yusuf Idris, mai taimaka wa Gwamna Bello Matawalle a harkar yada labarai, ya shaida wa manema labarai haka da yammacin ranar Lahadi cewa har yanzu ana ci gaba da kokarin ganin an sake su.

Gwamnatin ta Zamfara ta yi wannan bayani ne biyo bayan rahotannin da kafafen yada labarai suka bayar cewa an sake ‘yan matan.

Yusuf Idris ya ce gwamnan ya kammala ganawa da sarakunan gargajiya a jihar ne a gidan gwamnati da ke Gusau don ganin an dawo da daliban lafiya.

Anashi ɓangaren Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abutu Yaro, shi ma ya ce har yanzu ba a sako ‘yan matan ba. “Ina so in ja hankalin mutanen kirki na jihar Zamfara, ya kamata su yi watsi da duk wani labarin karya game da sakin daliban GGSS Jangebe da wasu jaridu ke yaɗawa.

“Ba gaskiya bane. “Amma, Alhamdulillah, gwamnatin jiha da jami’an tsaro suna iya bakin kokarinsu,” ya ce a cikin wani gajeren sakon da ya gabatar ga manema labarai a Jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Yusuf Idris, ya kuma bukaci jama’a da su yi watsi da rahotannin da kafafen yada labarai ke yadawa cewa an saki daliban, yana mai kira ga iyayen yara da mazauna jihar da su yi addu’ar Allah ya dawo da daliban lafiya.

Jami’in ya ce “Gwamnatin jihar ta himmatu domin dawo da daliban lafiya ko ba jima ko ba dade, ya kamata mu yi hakuri,” in ji jami’in.

Labarai Makamanta