Hanyoyin Sadarwar Zamani Na Da Rawar Takawa Wajen Bunkasa Kasa – CITAD

Cibiyar bunƙasa ilimin kimiyya da cigaban zamani CITAD ta yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da bada gudunmawar da ta dace wajen inganta hanyoyin sadarwar zamani domin cigaban kasa.

Babban Darakta na Cibiyar Yunus Zakari Ya’u ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da jawabi a taron manema labarai da cibiyar ta kira a Kaduna.

Ya ƙara da cewar kashi na 16 na taron haɓaka tsarin amfani da Internet na ƙasa da ƙasa da aka gudanar a kasar Poland ya tabbatar da tasirin da ilimin kimiyyar hanyoyin sadarwar zamani ke dasu, wajen kawo sauyi a ƙasa.

“A halin da muka tsinci kanmu yanzu a Najeriya da akwai koma baya sosai da jama’a ke fama dasu ta fuskar kimiyyar hanyoyin sadarwa, inda bincike ya nuna sama da rabin jama’ar Najeriya na fama da jahilcin wannan ilimi, kuma lamari ne wanda ba za a lamunta ba ya zama dole a yi wa tufkar hanci”.

“A halin da muke ciki yanzu da akwai al’ummomi kimanin 114 a tarayyar Najeriya wadanda hanyoyin Sadarwar zamani sun yi rauni ko kuma babu su gaba daya a yankin, wanda hakan ke nuna cewa ba su cikin tsarin cigaba na zamani kenan gaba daya”.

Yunus Zakari Ya’u ya cigaba da cewar akwai bukata da kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya kaimi wajen samarwa da inganta hanyoyin sadarwa domin cike wannan gibi da magance matsalar da hakan ke iya haifar wa.

Cibiyar ta kuma yi kira ga Ministan Sadarwa ya yi gaggawar samar da tsari da ƙirƙirar wasu sabbin hanyoyin sadarwar waɗanda za su taimakawa al’ummar Najeriya fita daga halin koma baya da suke ciki zuwa sabuwar duniya.

Sannan sun bukaci hukumar NCC ta fitar da wasu tsare tsare da dokoki wanda za su taimakawa wajen samar da hanyoyin sadarwa a dukkanin faɗin ƙasar, da kuma ba jama’a damar shiga cikin tsarin yadda kowa zai amfana.

Cibiyar ta kuma yi kira ga dukkanin masu rike da madafun iko tun daga kan masu muƙaman siyasa da sauran masu sarautu da su bada goyon baya wajen cimma wannan burin da ake dashi.

Labarai Makamanta