An bayyana cewar Najeriya na yin asarar kwata na kasafin kudinta da yakai kimanin Naira Triliyan Biyu da rabi duk shekara ta sanadiyyar cin hanci da rashawa.
Ƙungiyar ƙididdiga da kariya daga zamba ta ƙasa (SFAFP) ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar.
Ƙungiyar ta bayyana cewar ana samun faruwar hakan ne ta hanyar amfani da kayayyaki gwamnati ta haramtacciyar hanya da ƙin biyan haraji da kayayyakin da ake shigowa da su.
Ƙungiyar ta cigaba da cewar sauran hanyoyin sun hada da zamba gami da ƙwange da biyan albashi ga ma’aikatan bogi bayar da cin hanci gami da aringizo da sauran badaƙaloli masu yawa.
Shugaban kungiyar Iliyasu Gashinbaki yace kungiyar zata taimaka wajen fallasawa da bankado dukkanin wata badaƙala da ake amfani dasu wajen ha’intar gwamnati.
Gashinbaki ya kara da cewar cuwa cuwar ba wai kawai a Najeriya ake samun ta ba, ta haɗa da sauran ƙasashen nahiyar Afirka.
Ya bayyana cewar a wani bincike da aka gudanar a kwanan nan ya nuna cewa mafiyawan kasashen Afirka na fuskantar matsalolin taɓarbarewar arziki da tarin basussuka ne biyo bayan yadda cin hanci da rashawa rashawa ke illa ga ‘yan kuɗaɗen da suke samu.
You must log in to post a comment.