Haduwar Atiku Da Tinubu Ba Ta Siyasa Ba Ce – APC

Biyo bayan ra’ayoyi daban-daban da suka bayyana kan ganawar da babban jigo a jam’iyyar APC na kasa Bola Tinubu da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja a ranar Juma’a, 28 ga watan Mayu, jam’iyyar mai mulki ta mayar da martani kan surutan da suka biyo baya.

Mun kawo muku rahoto a baya cewa wasu masu amfani da shafin Twitter sun dage cewa taron shugabannin biyu bazai rasa nasaba da takarar shugabancin kasar na 2023 ba.

Da take martani a kan jita-jitar, APC, ta yi magana kai tsaye a ranar Asabar, 29 ga Mayu, ta shafinta na Twitter, @APCUKingdom, cewa Tinubu ya yi haduwar bazata ne da Atiku a filin jirgin sama.

Hakanan jiga-jigan biyu sun isa filin jirgin saman a kusan lokaci guda kuma sun gaisa cikin girmamawa kafin suka ci gaba da tafiyarsu mabanbanta.

A cewar jam’iyyar, gajeren ‘taron’ ba a shirya shi ba, ta kara da cewa Asiwaju Tinubu ba ya cikin ayarin masu tarbar tsohon mataimakin shugaban kasar zuwa gida Najeriya. Rubutun ya zo kamar haka:

“Wani sakon da Reno Omokri @renoomokri ya wallafa a shafinsa na Twitter da karfe 6:24 na safe a ranar 29 ga Mayu, 2021, wanda aka yiwa bidiyon take da:” Tinubu Ya Tarbi @atiku a filin jirgin sama yayinda tsohon mataimakin shugaban kasar ya dawo Najeriya “. “Wannan shi ne don sanar da jama’a cewa bayanan da ke kunshe a cikin rubutun da aka ambata a sama karya ne, kuskure ne, kuma shiryayye ne daga masu yada labaran karya don yaudarar ‘yan Najeriya, neman suna da kuma samun karramawa da bai dace ba.”

“Mai girma, tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar sun hadu a daren ranar 28 ga Mayu, 2021 a filin jirgin saman ba zato ba tsammani!”

Dole ne ‘yan Najeriya suyi watsi da ikirarin Reno Omokri sannan Jam’iyyar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da abin da ta kira karanbani da wallafar neman suna wanda Reno Omokri ya kirkira.

Ta kara da cewa: “Muna rokon ‘yan Najeriya da su yi watsi da kananan maganganu, da kuma wallafar neman suna da Reno Omokri wanda aka fi sani da Wendell Smith yayi mun gode.”

A baya mun ji cewa, ‘Yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta game da bayyanar hotunan Jigon jam’iyyar mai mulki taAPC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, lokacin da ya karbi bakuncin jigon jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja.

Labarai Makamanta