Hadakar Majalisun Dokoki Sun Yi Zaman Gyaran Kundin Tsarin Mulki

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa kwamitin da ke nazarin gyara kundin tsarin mulkin kasa na majalisar dokokin ya shirya taro da ya gayyato shugabannin majalisun jihohi 36 saboda a samu amincewar majalisun dokokin a gyare gyare 51 da kwamitin ya riga ya yi a kundin tsarin mulkin kasar.

A hirar shi da manema labarai dangane da wannan zaman, Sanata Uba Sani ya ce wannan kundin tsarin mulkin ya dade ba a yi gyara ba, shi ya suka zauna da majalisar dattawa da majilar dokokin don su tattauna domin a gyara don cimma matsaya daya. Dole sai da hadin kai kafin a samu gyara.

Ganin cewa gyaran kudin tsarin Mulkin ba zai yiwu ba, sai an samu kashi biyu bisa uku na Majalisun dokokin da na jihohi, kakakin Majalisar dokokin Jihar Neja Abdullahi Bawa Wuse ya ce dole ne a ba kowa dama ya bayyana ra’ayin sa.

A nashi bayanin, shugaban kwamitin duba kundin tsarin mulkin kasa kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa Ovie Omo Agege ya yaba wa Ofishin raya kasa da Kungiyar Tarayyar Turai a bisa goyon bayan su.

Labarai Makamanta