Gwamnonin Arewa Sun Sha Alwashin Shawo Kan Matsalar Tsaro Dake Addabar Yankin

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa Kungiyar Gwamnonin Arewa a bisa irin matakan da suke dauka na ganin sun kawo karshen matsalolin tsaro da ya addabi yankin baki daya.

Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin Shugaban ma’aikatan fadan Gwamnati Ibrahim Gambari, a yayin da ya wakilci shugaban ƙasa wajen buɗe taro kan matsalar tsaro da tattalin arziki Gwamnoni da Sarakunan Arewa suka shirya a Gidan Gwamnati na tunawa da Sir Kashin Ibrahim dake Kaduna.

Buhari ya bayyana cewa, duk da kokarin da Gwamnonin Arewan ke yi, ya zama wajibi a gare su, da su kara tashi tsaye wajen ganin sun tunkari babban matsalar tsaron da taki ci yaƙi cinyewa dake addabi Al’ummar yankin baki daya.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana irin gudunmuwar da Gwamnatinsa ke bayarwa babu dare ba rana kan harkokin tsaro domin ganin an fatattaki ‘yan ta’adda dake cin karen su babu babbaka a Yankin na Arewa.

A nashi jawabin, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewan, kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya bayyana cewa sun shirya wannan taron ne na masu ruwa da tsaki domin zakulo hanya ingantaciya da zasu bi domin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankin Arewa.

Gwamna Lalong ya ƙara da cewa, daga cikin abin da suka tattauna a kai, sun haɗa da, matsalar tsaro da kuma cin ma matsaya wajen ganin daukacin Gwamnonin Arewan sun Gina da samar da labukan kiwon shanu domin samarwa Fulani makiyaya wuraren da zasu dinga kiwon shanu.

Gwamnonin Arewan sun kuma bukaci takwarorinsu Gwamnonin kudancin kasar nan, da su guji yin duk wani kalamai da zai kai ga tunzura Al’ummar kasar nan cikin fitina, domin a cewarsu, Nijeriya kasar kowa da kowa ne, kuma dokar kasa ta bai wa kowane Ɗan Nijeriya ‘yan cin zama a duk inda yakeso, batare da muzgunawa da cin zarafi ba.

Tun farko da yake jawabi Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Elrufai, bayyana cewa, yanzu ba lokaci bane na musayar yawu, ko korafe-korafe a tsakanin Gwamnonin. A cewar sa, Al’ummar da suke mulka sun zura masu Ido saboda nauyin hakƙokinsu dake rataye a wuyansu. saboda haka ya zama wajibi a gare su da su yi mai yiwuwa wajen ganin sun kawo karshen matsalolin tsaro da suke addabar yankin.

A jawabin mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar ya tunatar da gwamnonin cewa dukkanin idanuwan jama’ar ƙasar na kansu, domin ganin yadda za suyi da matsalar tsaro dake neman gurgunta yankin.

Suma anasu ɓangaren Ƙungiyar Dattawan Arewa ta bakin Sakataren Ƙungiyar Dr. Hakeem Baba Ahmed sun yi gargadi ga gwamnonin cewa sha’anin tsaro babbar harka ce saboda haka su daina hantarar juna a bainar jama’a.

Daga ƙarshen taron, Gwamnonin da Sarakunan Arewa sun fitar da matsayarsu kamar haka;

Sun shawarci Gwamnatin Tarayya da lalle ta samar da kariya da ingantaccen tsaro ga duk Makarantun dake faɗin Arewacin kasar nan.

Sannan sun kafa wani kwamiti wanda aka ɗaura ma alhakin samar da wata gidauniya ta musamman domin tallafa ma wadanda ibtala’in rikici ya rutsa da su, da sake gina ma ‘yan gudun hijira dake yankin Arewa matsugunni.

Gwamnonin sun yarda zasu hada kai da Gwamnatin Tarayya wajen samar da Jami’an tsaro na civilian JTF, domin taimaka ma sauran Jami’an tsaro dake aiki a jihohin nasu.

Sannan sun bayar da shawarar cewa, ya zama wajibi a haɗa kai da da kuma baiwa Sarakunan Gargajiya dama domin bayar da tasu gudunmuwar wajen inganta harkar tsaro a faɗin yankin.

Sannan sun bayyana cewa, wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta tsaurara matakan tsaro wajen hana shigowa da muggan makamai ta ko Ina a faɗin kasar nan.

Sun bayyana cewa dole ne Gwamnatin Tarayya ta fitar da wata hanya da za’a sami daidaituwa tsakanin manoma da makiyaya domin magance matsalar rikice-rikice a faɗin kasar nan.

Labarai Makamanta