Gwamnonin Arewa Sun Kyamaci Gina Makarantun Almajirai Da Na Yi – Jonathan

A jawabi da ya gabatar a taron yaye dalibai a cibiyar ilimin tsaro ta NISS da ke Abuja a ranar Alhamis, Jonathan ya kwatanta Almajirai a matsayin abin da ka iya zama matsala a gaba idan ba a dauki mataki na kula da su ba.

Jonathan ya ce wasu gwamnonin arewa ba su ji dadi ba a lokacin da ya gina wa Almajirai makarantu.

Ya bukaci gwamnonin jihohin arewa 19 da su gyara tsarin ilimin Almajiri don kawo gyara akan rashin tsaron da kasar nan ke fuskanta. Jonathan ya ce akwai bukatar gwamnoni su zage damtse wurin yin ayyuka.

Jonathan ya kara da cewar ya zama wajibi gwamnoni su yi aiki tukuru don ba aikin gwamnatin tarayya bane gini da kulawa da makarantu.

“Wata matsalar da ke damunmu ita ce ta rashin tsaro. A Afirka, me yasa muke da matasa marasa ayyukan yi? Akwai yuwuwar rashin aikin yi ne ke kawo ta’addanci.

“Hanyoyin shawo kan rashin aikin yi akwai matsalar ilimi. Kamar yadda Nelson Mandela ya ce, idan ka ba mutane ilimi ka ba su makamin sanin abinda ke faruwa a yankinsu. “Ilimi mabudi ne, don haka idan ba ma da ingantaccen ilimi, dole matsaloli su yi ta barkwewa ta ko ina.”

A cewarsa ilimantar da matasa ce mafita ga matsalar tsaro Ya kara da cewa idan kasa bata dage wurin bunkasa matasa ba, sai shugabanni sun kashe kudade wurin kulawa da matsalar tsaro.

Akwai hanyoyi da dama da gwamnati za ta bi amma sai gwamnoni sun yi aiki tukuru wurin inganta makarantu don ba aikin gwamnatin tarayya bane, inji tsohon shugaban kasan.

Ya kara da cewa lokacin da ya yi kokarin gyara ilimin almajirai, ta yiwu wasu gwamnonin ba su ji dadi ba, amma ba su sanar da shi hakan ba har sai da ya sauka daga kujerarsa.

Labarai Makamanta