Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Matsayarsu Akan Pantami

Ƙungiyar gwamnonin arewa ta nesanta kanta da duk wata kalar cece-kuce da wasu ‘yan Najeriya keyi kan kalaman da Ministan Sadarwa Pantami yayi a baya masu nasaba da harkar tsaro.

A ruwaito ƙungiyar gwamnonin arewa sun bayyana cewa ba laifi bane idan Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani ya faɗi ra’ayinsa. A jawabin ƙungiyar tace Ministan ya wanke kansa inda yayi martani a kan lamarin, kuma martaninsa ba ya buƙatar bincike ko kuma ƙin amincewa domin yayi cikakke bayani.

“Ministan ya fito ya kare kansa, kuma jawabinsa baya buƙatar bincike ko kuma ƙin amincewa.” Hakanan ƙungiyar gwamnonin tace ta gano wani labari da a ke yaɗawa a kafafen sada zumunta domin ɓatawa gwamnonin yankin arewa suna, inda ake yaɗa jita-jitar cewa suna goyon bayan kalaman da Dr. Pantami yayi a baya.

Ƙungiyar tayi kira ga al’umma da suyi watsi da duk wani labari da suka gani a na yaɗawa a kafafen sada zumunta domin a ɓata musu suna.

Hakanan, Isa Pantami, yayi zargin cewa duk waɗannan abubuwan dake faruwa akansa shirayayyu ne, kuma an shiryasu ne domin a ɓata masa suna.

Labarai Makamanta