Gwamnonin Arewa Cima Zaune Ne – Hauwa Kabir

An bayyana Gwamnonin Yankin Arewa a matsayin wasu cima zaune wanda basu damu da sha’anin Al’ummar Yankin su ba.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shahararriyar Yar Gwagwarmayar nan da kare maradun Al’ummar Arewa, Kwamared Hauwa Kabir, a cikin wata takardar sanarwar da ta sanyawa hannu kuma aka raba ma manema labarai a kaduna.

Kwamared Hauwa Kabir, ta ƙara da bayyana cewa, “Abin da ke faruwa a kasar nan babban abin takaici ne, domin an raina Al’ummar Yankin Arewa, an mayar da mu tamkar wasu wadanda basu san abin da suke yi ba. Kowa ya kwaso kashinsa sai ya shafa ma Al’ummar Yankin Arewa.”

A cewar ta, ” ko daga baya bayan nan ,tarihi ba zai taba mantawa da irin gudunmuwar da Al’ummar Arewa suka bayar ba, su kansu Kabilar Yarbawa sun san da haka. Misalin lokacin zaben Obasanjo, mafi yawancin Kabilar Yarbawa sun juya ma Obasanjo baya, sun kyamace shi, sun jiya masa ba, amma mu ‘yan Arewa mune mukayi ruwa muka yi tsaki, har Allah ya tabbatar da Obasanjo a matsayin Shugaban kasa a wancan lokacin. Amma abin mamaki da takaici, ko shekara daya Obasanjo bai yi a kan mulki ba a lokacin, babu irin cin kashin da Kabilar Yarbawa basu yi ma Al’ummar Arewa dake zaune a Yankin kudu ba, ko a lokacin Obasanjon da sauran manyan Yan Yankin kudun suka yi kyememe suka shafa ma fuskarsu toka akan lamarin.”

Kwamared Hauwa Kabir ta ƙara da bayyana cewa, ” Su kuma shugabannin mu na Arewa sun zama tamkar wasu cima zaune, wanda babu abin da ya shafe su da lamarin Al’ummar su, illa idan ka gansu suna taron gaggawa, to tabbas wata matsalarsu ce ta taso, wanda suke son shugaban kasa ya biya masu. Sun fi damuwa da lamarin kudin Paris club, ko state allocation, fiye da jini ko dukiyar Dan Arewar dake zaune a kasar nan ba.”

“Saboda haka, ina kira da babban murya ga Shugabannin Yankin kudancin kasar nan, da lalle ya zaman masu wajibi su tashi su dauki mataki mai karfin akan Matasansu, wadanda suke kashe mana Yan uwa babu gaira babu dalili. Wallahi, wallahi, wallahi kura ta fara kai mu bango, mun gaji da cin kashin da su ke mana haka!”

Kwamared Hauwa Kabir ta ce, “su kuma masu kiran kansu da sunan jagororin Arewa, ina kira a garesu da cewa, su tuna fa, ba irin wanna bane tubalin da su Sardauna suka daura su a kai, domin a halin yanzu sun ci amanar Arewa da kuma Al’ummar Arewa. Sun bari wasu tsirarrun kabilun kasar nan na cin karansu babu babbaka ga duk wani Dan Yankin Arewa dake zaune a Yankin kudancin kasar na. Kar fa su manta da cewa, Nijeriya kasar kowa da kowa ce, kuma dokar kasar nan ta baiwa kowa ‘yan din damar zama a duk inda yakeso a cikin fadin kasar nan. A cewarta.

Labarai Makamanta