Gwamnoni Za Su Goyi Bayan Cire Tallafin Man Fetur – El Rufa’i

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ce a shirye gwamnatocin jihohi suke su goyi bayan gwamnatin tarayya wajen cire tallafin man fetur baki daya.

An ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Talata a wajen gabatar da sabbin bayanai na Bankin Duniya reshen Najeriya da aka gudanar a Abuja.

El-Rufai, wanda ya yi bayani ta intanet, ya ce idan ba a cire tallafin man baki daya ba, watakila jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashi a shekarar 2022 ba.

A cewarsa, an dade da cire tallafin kalanzir, wanda shi ne ya fi yi wa talakawa amfani ba tare da wata matsala ba, yayin da aka cire tallafi a kan gas wanda manyan motoci suka fi yin amfani da shi.

Labarai Makamanta