Gwamnoni Sun Yi Nasara A Karar Da Suka Kai Shugaban Kasa Kotu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a ranar Juma’a ce Babbar Kotun Tarayya ta dakatar da Gwamnatin Tarayya kwasar dala miliyan 418 daga asusun jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774, da nufin ta biya wasu dillalan gada-gada masu iƙirarin cewa sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi ayyukan adadin kuɗaɗen a shekarun baya.

Dillalan gada-gadar sun ce sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi aikin tuntuɓa ne da wasu kwangiloli tsakanin 1995 da 2002, wajen ƙoƙarin aikin dawo masu da kuɗaɗen da aka riƙa ɗibar masu ana biyan bashin Paris Club da London Club.

Babban Mai Shari’a Iyan Ekwo ya umarci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da fara kwasar kuɗaɗen da ta shirya fara kwasa daga watan Nuwamba, har sai bayan an kammala shari’ar da Gwamnonin Najeriya 36 suka shigar a gaban sa.

Gwamnonin 36 sun shigar da ƙarar ta hannun gogaggun lauyoyin su biyu, Jibrin Okutedo da Ahmed Raji, waɗanda dukkanin su manyan lauyoyi ne (SAN).

A ƙarar da su ka shigar, lauyoyin sun shaida wa kotun cewa Gwamnoni 36 na Najeriya ba su yarda cewa waɗancan dillalan gada-gadar sun yi ayyukan da su ka ce sun yi a jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774 a shekarun baya ba.

Lauyoyin sun ce masu iƙirarin sai an biya su haƙƙin kuɗaɗen har dala miliyan 418, ‘yan gidoga ne kawai, lamarin babu gaskiya a ciki.

“Kuma idan Gwamnatin Tarayya ta kwashi kuɗaɗe a asusun jihohi 36, to jihohin za su kasance a talauce, ta yadda biyan albashi ma ba zai yiwu ba.”

Daga cikin waɗanda gwamnoni 36 su ka kai ƙara, har da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ta Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Shari’a da Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a da kuma Ofishin Bin-diddigin Kuɗaɗen Bashi (DMO) da kuma Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Kasa na Gwmnatin Tarayya, wato FAAC.

Cikin watan Agusta ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya yi biris da shawarar gwamnonin Najeriya, ya rattaba hannun amincewa a biya ‘yan gada-gadar su shida dala miliyan 418, kwatankwacin fiye da Naira biliyan 170.

Hannun da Buhari ya rattaba ne ya sa Ministar Harkokin Kuɗaɗe ta umarci Ofishin Kula da Basussuka na Ƙasa (DMO) cewa ya bai wa ‘yan gada-gadar takardun alƙawarin biyan su basussukan cikin shekaru 10.

Gwamnonin Najeriya 36 sun rubuta wa Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed Wasiƙa, inda su ka gargaɗe ta cewa kada fa ta sake ta biya dala miliyan 418 ga ‘yan kwangilar da gwamnonin su ka ce ‘yan gidoga na gidi.

Wasiƙar dai sun rubuta ta ne ta hannun lauyan su Femi Falana, wanda ya rubuta mata hatsarin da ke tattare da biyan kuɗaɗen.

Falana ya nemi a madadin gwamnonin cewa Minista Zainab ta janye umarnin da ta ba Ofishin Kula da Basussuka (DMO) cewa ya fara shirin bayar da takardun alƙawarin biyan kuɗaɗen a cikin wasu ƙayyadaddun lokuta ga ‘yan kwangilar.

Gwamnonin sun ce ya kamata Minista Zainab ta fahimci cewa sun shigar da ƙara a Kotun Ƙoli, kuma Kotun Ƙoli ba ta ce a biya kuɗaɗen ba, domin harƙalla ce da dungu da gidoga kawai.

Kuɗaɗen waɗanda dala miliyan 418 ne, idan aka canja su zuwa dala a farashin gwamnati na dala 1 Naira 410, za su kama naira biliyan 171 kenan.

Waɗanda za a biya kuɗaɗen dai su shida sun haɗa da tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ned Nwoko, wanda ya ke kafa hujja da umarnin biyan wanda Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bayar a ƙarar da su ka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/148/2017.

Sai kuma wasu mutum uku da ke neman a biya su dala miliyan 143,463,577.76 a ƙarar da su ka shigar mai lamba FHC/CV/2129/2014.

Su ukun sun haɗa da Riok Nigeria Ltd, Orji Nwafor Orizu da wani mai suna Olaitan Bello.

Akwai kuma kamfanin wani mai suna George Uboh, wanda zai karɓi dala miliyan 47,831,920.

Gwamnonin sun nuna damuwa kan yadda Minista Malami ya ƙi jin gargaɗin zargin harƙalla, ya riƙa ƙoƙarin a biya bashin naira biliyan 159.

An shafe shekaru ba ɗaya ba, ba biyu ba, Ministan Shari’a Abubakar Malami na bijire wa gargaɗin da ake yi masa cewa wasu kuɗaɗe da ya ke ta ƙoƙarin ganin an biya daga cikin kason kuɗaɗen Jihohi da Ƙananan Muhumomi har dala milyan 418 (naira biliyan 159), akwai gidoga a cikin lamarin.

Amma duk da gargaɗin da aka rika yi wa Malami, ciki kuwa har da rahoton da EFCC ta damƙa masa, wanda ta nuna cewa bashin haramtacce ne, ba gaskiya ba ne, shi kuma Minista Malami ya rufe ido sai matsa lamba ya ke yi domin ganin an biya waɗanda aka ce wai su na bin bashin, ta hanyar riƙa cirar kudade ana biyan bashin daga kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke bai wa Johohi da Ƙananan Hukumomi a duk ƙarshen wata.

Sauran mutane biyun da su ka haɗa kai da Minista Malami domin ganin an biya kuɗaɗen ido-rufe, sun haɗa da Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari da kuma Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed.

Batun wannan bashi da ake tankiya da tababar sa, ya samo asali ne daga wani hukuncin da kotu ta yanke cewa wasu ’yan kwangila da jami’an tuntuɓa na bin jihohi da ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan basussuka.

Labarai Makamanta

Leave a Reply