Gwamnoni Sun Bukaci Sabon Shugaban ‘Yan Sanda Ya Kawo Ƙarshen ‘Yan Ta’adda

Kungiyar Gwamnonin Arewa sun yi kira gami da neman sabon Shugaban rundunar ‘yan sandam Najeriya Usman Alkali, da yayi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin tsaro ya dawo a kasar nan musanman yankin Arewa.

Shugaban kungiyar gwamnonin na Arewa kuma Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ne ya yi kiran a ranar Asabar, 10 ga Afrilu, a cikin sakon taya murna ga sabon shugaban ‘yan sandan, da ƙungiyar gwamnonin ta fitar.

A cikin wata sanarwa ta bakin mai magana da yawunsa, Makut Macham, ya ce Alkali ya cancanci wannan sabon matsayin duba da yadda ya yi wa kasar hidima. Ya yi alkawarin cewa gwamnoni daga yankin za su ba da goyon bayan da ya dace ga sabon Shugaban yan sandan.

“A matsayin mu na gwamnonin arewa, muna nan kan bakan mu na kula da harkokin ‘yan sanda da duk wani matakin da zai kai mu ga tabbatar da tsaron yankin mu wanda yake fama da matsalolin rashin tsaro”.

“Dole ne mu hada kai don daukar sabbin matakan da za su ba mu damar shawo kan wadannan kalubale kuma mu ci gaba da kasancewa a kan halin da ake ciki ta hana masu aikata laifuka aiwatar da munanan ayyukansu.” Inji Gwamnonin

Labarai Makamanta