Gwamnoni Sun Bukaci Gwamnatin Buhari Ta Yi Aman Biliyoyin Kudin Haraji

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnoni 36 na kasar nan sun maka Ministan shari’a, Abubakar Malami a kotu, a matsayinsa na babban lauya kuma mai wakiltar gwamnatin tarayya.

Rahoton yace gwamnatocin sun roki kotu ta tursasa wa gwamnatin tarayya ta dawo masu da sama da Naira biliyan 176 da aka tara daga 2016 zuwa 2020.

A cewar gwamnatocin, jihohi ne suke da ikon karbar kudin hatimi ba jami’an gwamnatin tarayya ba.

Har ila yau, kwanishinonin shari’ar a madadin gwamnoni, suna so kotu ta bayyana cewa ko Abubakar Malami SAN yana da hurumin taba kudin.

An shigar da karar mai lamba SC/CV/690/2021 ne a kotun koli. Ana neman Alkalai su raba gardama kan abin da sashe na 4(2) na dokar harajin yace.

Kwamishinonin shari’a na jihohin Najeriya suna ikirari cewa a dokar kasa ba gwamnatin tarayya aka ba nauyin karbar kason harajin hatimi a cikin jihohi ba. Shari’ar za ta raba gardamar ko gwamnatocin jihohi suna da hakkin 85% a cikin kason duk wani harajin hatimi da aka samu daga kudin da aka aika ta banki.

Hakan zai sa a hana duk wani jami’in gwamnatin tarayya karbar wannan haraji. Har zuwa yanzu, ba a sa ranar da za a soma sauraron wannan a kara a kotu ba.

Idan kwamishinonin sun dace a kotu, za a bar kowace jiha ta ci gashin kan-ta, ta karbi harajin da aka tara a jiharta daga kudin da suka shiga asusun bankuna.

Labarai Makamanta

Leave a Reply