Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta dora alhakin katutun talaucin da ke damun Najeriya kan gwamnonin jihohi.
Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Clem Agba ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya ranar Laraba, kamar yadda gidan talbijin na Channels TV ya rawaito.
Ya ce shirin gwamnatin tarayya na kyautata rayuwar ‘yan kasar bai yi tasirin da ya kamata ba ne saboda gwamnonin jihohi ba su bai wa gwamnatin tarayya hadin kai ba.
Mr Agba ya kara da cewa gwamnonin sun fi mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan da ba su da muhimmanci, maimakon inganta rayuwar al’ummar karkara.
A wani labarin na daban Gwamnonin Najeriya 36 sun sake maka Gwamnantin Shugaba Muhammadu Buhari ƙara a Kotun Ƙoli, inda su ke neman kotu ta tilasta wa Gwamnatin Tarayya ta maida masu kuɗaɗen harajin naira biliyan 176 da Gwamnatin Tarayya ta karɓa a hannun mutane a faɗin jihohin ƙasar nan.
Maƙudan kuɗaɗen da ake tankiya a kan su ɗin dai Gwamnatin Tarayya ta karɓe su ne tsakanin 2015 zuwa 2020 a jihohin Najeriya, da sunan ‘Harajin Stamp Duties’.
Harajin ‘Stamp Duties’ dai wasu kuɗaɗe ne da Gwamnatin Tarayya ke tatsa a jikin kowane ɗan Najeriya, a duk jihar da ya ke idan ya ciri kuɗi a asusun sa na banki, ko kuma ya tura kuɗi a wani asusu daga asusun ta, ko ta waya, ko ta POS ko ta na’urar ATM ko kuma kai-tsaye daga cikin banki.
Waɗannan kuɗaɗen ne jihohin Najeriya su ka ce kowace jiha ke da haƙƙin karɓar su a jihar ta, ba haƙƙin gwamnatin tarayya ba ne karɓar kuɗaɗen.
Bisa wannan dalili ne kowane Antoni Janar na jihohi 36 ya shigar da ƙara a madadin jihar sa a Kotun Ƙoli. Kuma kowace jiha ta ɗauki lauyan ta, inda su ke neman Gwamnatin Tarayya ta maido masu jimlar Naira biliyan 176 da ta tatsa a cikin jihohin ƙasar nan daga 2015 har zuwa ƙarshen 2021.
Wannan dambarwa ta taso a daidai lokacin da Babbar Kotun Tarayya ta Fatakwal ta haramta wa Gwamnatin Tarayya karɓar Harajin VAT a Jihar Ribas, inda kotun ta ce harajin VAT haƙƙin gwamnatin jiha ne, ba na gwamnatin tarayya ba ne.
Tuni ita ma jihar Legas har Majalisar Dokokin ta sun kafa dokar daina biyan VAT ga Gwamnatin Tarayya a Jihar Legas, sai dai a riƙa biya ga gwamnatin jiha.
Haka kuma wanann dambarwa ta zo ne wata ɗaya bayan Gwamnatocin Jihohi 36 sun kafsa jayayya da Gwamnatin Tarayya kan batun biyan wasu ‘yan gidoga Naira biliyan 171 daga asusun jihohi da ƙananan hukumomi.
You must log in to post a comment.