Gwamnoni Ne Matsalar Najeriya Ba Shugaban Ƙasa Ba – Kalu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan Abia, Orji Kalu ya zargi gwamnonin Najeriya da bari har matsalar tsaro ya kai matsayin da ya ke yanzu.

Kalu a tattaunawa da yayi da Arise TV ya ce gwamnoni ne suka fi kusa da mutane, sun san masu aikata ta’addanci a jihohin su.

” Idan gwamnoni za su mike tsaye su yaki matsalar tsaro a johohinsu toh lallai su bada himma, domin shugaba Muhammadu Buhari ya yi iya kokarin sa.

” Buhari ba zai zo jihohin su ya yi musu yaki da ƴan ta’adda ba, sune za su mike tsayi su tabbatar sun yake su.

Kalu ya kara da cewa gwamnoni da yawa ba su takarawar gani ba wajen kawo karshen matsalar tsaro a jihohin su, ” kowa Buhari amma kuma sune suka fi kusa da waɗannan ƴan ta’addan amma kuma ba su yin komai a kai.

” Gwamnati Buhari ta taka rawar gani matuka, abin da ya ke faruwa a kasarnan a mulkin baya, da Buhari bai zo ba da kila tuni an manta da anyi wata kasa wai Najeriya.

” Wannan shine gaskiyar magana. Amma kuma ya zo ya zage damtse ya tambatar an kawo karshen matsaloli da dama musamman a fannin matsalar tsaron ƙasar nan.

A karshe Kalu ya ce matsalar ƴan bindiga da suka addabi mutane a Najeriya matsalace da ke neman a kashe kuɗi ma su yawa kuma gwamnati na kokarin haka.

Labarai Makamanta