Gwamnoni Ne Matsalar Dimokuradiyya A Najeriya – Ghali Na’abba

Tsohon shugaban Majalisar wakilan tarayya Ghali Umar Na’Abba ya zargi gwamnonin jihohi da zama barazana ga mulkin dimokiradya saboda matakan da suke dauka wadanda suka saba ka’ida.

Na’Abba ya zargi gwamnonin da karbe iko da jam’iyyu wajen zama wuka da nama ta hanyar yin gaban kansu wajen bayyana wanda zai tsaya takarar zabe ko kuma wanda zasu nada domin rike mukamai daban daban.

Tsohon shugaban majalisar yace tun daga shekarar 1999 gwamnonin suka zama kadangarun bakin tulu, wadanda suke taimakawa wajen murkushe dimokiradiya a cikin gida, abinda ke hana gabatar da yan takarar da suka fi cancanta domin tsayawa zabe.

Na’Abba yace ko zaben fidda gwani wasu gwamnonin basa bari ayi, sai dai dauki dora ko kuma suce za’ayi sasanci domin gabatar da wadanda zasu tsaya zabe.

Tsohon shugaban majalisar yace muddin ana bukatar tabbatar da dimokiradiya a Najeriya, ya zama wajibi a aiwatar da sauyi wajen baiwa kowa dama wajen shiga zaben fidda gwani da kuma tsayawa takara domin baiwa jama’a damar zabin abinda suke so, amma ba abinda gwamnonin suke so ba.

Labarai Makamanta