Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Gwamnoni A Nemi Mafita: Asusun Gwamnatin Tarayya Ya Shiga Rudani – Hukumar Kula Da Dukiyar Gwamnati

Hukumar dake kula da kason albashi da kudin ma’aikata a Najeriya, ta ce ana damun asusun rabon dukiyar kasa watau FAAC. Ta yi gargadi cewa bukatun da su ke zuwa daga bangarorin gwamnatin tarayya, jihohi da na kananan hukumomi su na yi wa asusun FAAC yawa.

Shugaban hukumar na kasa, Injiniya Elias Mbam, ya yi kira ga gwamnatocin jihohin kasar da su fito da hanyoyin bunkasa samun kudin shigarsu. Elias Mbam ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi alkaluman jihohi na ASVI daga hannun Editan jaridar Economic Confidential.

Elias Mbam ya ce bukatun jihohi ya yi wa asusun kasar nauyi a dalilin dogara da jihohin su ke yi da FAAC. “Dogaro da aka yi da kason wata-wata daga asusun ya sa ya zama dole jihohi su bunkasa hanyar samun kudin shigarsu ta wasu hanyoyi na daban.

“Rahoton ASVI na shekara-shekara ya na bada bayanai, tare da taimakawa Hukumar wajen aikinta na kira ga jihohi su inganta kudin da su ke tatsa da kansu.” Mbam ya yaba da kokarin da jaridar Economic Confidential ta ke yi, musamman wajen fitar da bayanai da alkaluma masu muhimmanci da za su taimakawa harajin jihohi.

Editan Jaridar ya ce binciken da su ka yi ya nuna masu cewa jihohi da-dama ba za su iya gudanar da harkokin mulki ba, ba tare da kason da suke samu duk wata ba. Ya ƙara da cewar alkaluma sun tabbatar masu da cewa akwai jihohi bakwai da abin da su ke samu daga haraji na IGR bai kai kashi 10% na kudin da su ke karba daga kason tarayya ba.

“Jihohin Ribas, Kaduna, Enugu, Kwara da Zamfara ne kawai su ka yi hobbasa wajen samun kudin shiga a 2019, idan aka kamanta da abin da su ka samu a shekarar 2018″.

Exit mobile version