Gwamnatin Zamfara Za Ta Dauki Nauyin Gasar Karatun Al’kur’ani Ta Bana

Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala shirye-shirye don daukar nauyin gasar al-Qur’ani ta kasa wanda za a yi a ranar 16 ga watan Disamba na wannan shekara mai ƙarewa ta 2023.

Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a wajen bikin bude gasar al-Qur’ani na jihar wanda aka yi a Gusau a ranar Talata.

Nasiha ya bayar da tabbacin cewa a shirye gwamnatin jihar take ta bayar da duk gudunmawar da ake bukata na kudi don gudanar da gasar cikin nasara da ba baki masu halartan gasar kulawar da yakamata.

“A matsayin Zamfara ta jihar dake bin tafarkin shari’a, gwamnatinmu tana bayar da muhimmanci ga bangaren shari’a da kuma samar da duk abubuwan bukata don gudanar da gasar karatun Qur’ani na jiha da kasa baki daya cikin nasara a jihar.”

Da yake jawabi a taron, babban bako Dr. Atiku Balarabe, ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi koyi da koyarwar shari’a ta hanyar bayar da cikakken kulawa ga akin da za su zo jihar. Balarabe ya ce dole mu yi biyayya ga koyarwar Qur’ani a matsayin littafi mafi daraja don cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya.

Labarai Makamanta