Gwamnatin Zamfara Ta Sauke Sarkin Ɗansadau

Gwamna Bello Mohammed (Matawallen Maradun, Barden Hausa, Shattiman Sakkwato) ya Amince da dakatar da Sarkin Dansadau, Alhaji Hussaini Umar da gaugawa.

Kazalika Gwamnan ya Amince cewa Hakimin Dansadau, Alhaji Nasiru Muhammad S/Kudu da ya cigaba da kulawa da ayyukan Masarautar

Haka nan kuma an sakatar da Hakimin Nasarawa Mailayi Alhaji Bello Wakkala da gaugawa, Gwamnan ya kuma kafa Kwamiti Mai ƙarfi da zai binciki wadanda aka dakatar daga Muƙaman nasu.

Shugaban wannan Kwamitin dai shine mai ritaya DIG Muhammad Ibrahim Tsafe, sai membobin Kwamitin da suka haɗa da Hon. Yusuf Alhassan Kanoma, Hon. Ibrahim T. Tukur, Sheikh Ahmad Umar Kanoma, Sheikh Abdullahi Umar Dalla Dalla, Sheikh Umar Kabir Maru sai Sakataren Kwamitin Barrister Abdurasheed Haruna.

Gwamnan ya ja kunnen Jami’an tsaro tareda nanata cewa har yanzu dokar nan ta Shugaban ƙasa wadda tace duk wanda aka gani da Bindiga ba bisa ƙa’ida ba a harbe shi tana aiki a faɗin jihar.

©Zuma times Hausa

Labarai Makamanta