Gwamnatin Zamfara Ta Fara Safarar Shanu Daga Waje

Labarin dake shigo daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta kammala shirye-shiryen shigo da awaki da shanu daga kasashen Afirka ta Kudu da Norway a wani mataki na bunkasa matsugunan RUGA a jihar.

Gwamna Bello Matawalle ne ya sanar da hakan a garin Kaura-namoda yayin taron horas da masu ruwa da tsaki da kuma jajircewa kan ci gaban shirin RUGA da Rahusa Ventures ta shirya wanda Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya dauki nauyi.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan gandun daji da kiwo Dr. Ibrahim Abdullahi ya ce za a ajiye dabbobin a RUGA da ke karamar hukumar Maradun domin su zama abin koyi a kokarin gwamnatin jihar na bunkasa matsugunan RUGA.

“Tun daga nan mun ba da oda kuma dabbobin za su iso jihar nan ba da jimawa ba,.” Matawalle ya ce an kashe Naira biliyan 2.4 don gina RUGA a karamar hukumar Maradun, inda ya ce an kusa kammala aikin. Ya jaddada cewa an ware kudi naira biliyan 8.6 domin gina matsugunan RUGA guda uku a shiyyoyin sanatoci uku dake jihar.

Da yake jawabi, Shugaban taron, Dakta Abdullahi Maiwada, ya ce taron na da nufin horar da masu ruwa da tsaki kan yadda za su raya filayen kiwo na kansu domin gujewa rikici na Fulani makiyaya.

“An zabo mahalarta 250 daga kananan hukumomi uku na shiyyar Sanatan Zamfara ta Arewa wadanda akasari manoma, makiyaya, shugabannin gargajiya da na siyasa ne”.

Maiwada ya ce yayin da masu ruwa da tsaki za su iya shirya wuraren kiwo nasu, za a rage rikicin Fulani makiyaya da ‘yan bindiga da satar shanu ko kuma kawar da su gaba daya.

Ya yabawa Sanata Sahabi Yau bisa shirya taron bitar a matsayin wani bangare na ayyukan mazabar sa, inda ya yi kira ga daukacin ‘yan siyasar jihar da su yi koyi da shi.

Labarai Makamanta