Gwamnatin Tarayya Za Ta Yi Afuwa Ga Fursunoni Domin Rage Cunkoso A Gidajen Yari

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan harkokin cikin gida na ya ce yana shirin ganawa da gwamnonin jihohi 36 don cimma matsaya kan sakin aƙalla kashi 30 cikin 100 na fursunoni daga gidajen yarin da ake tsare da su a faɗin ƙasar.

Alhaji Rauf Aregbesola ya bayyana hakan lokacin da yake magana yayin wani taron ƙara wa juna sani da kamfanin labarai na Najeriya, NAN, ya shirya a Abuja.

Ministan ya ce yunƙurin ya zama dole saboda kashi 90 cikin 100 na mutanen, ana tsare da su ne sakamakon karya dokoki daban-daban na jihohin.

Haka nan, ya ce fiye da kashi 70 cikin 100 na fursunoni 75,635 da ake tsare da su yanzu haka jiran shari’a suke yi.

Ƙasa da kashi 10 cikin 100 ne kawai na fursunonin suka karya dokar gwamnatin tarayya, a cewar ministan.

“Rage cunkoso a gidajen yari 253 a faɗin Najeriya ya zama dole saboda bai kamata wasu daga cikin fursunonin su ci gaba da zama a gidan yari ba,” in ji shi.

Labarai Makamanta