Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Cibiyar Kula Da Tsofaffi – Ministar Jin Ƙai

Ministar Harkokin Agaji Da Jinkai, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya na nan ta na kokarin kafa cibiya ta musamman domin kulawa da halin da dattijai maza da mata su ke ciki a kasar.
A Turance, sunan cibiyar dai ‘National Senior Citizens Centre’.

Ministar bayyana wannan aniyar ne a lokacin da ta ke ganawa da wata kungiya mai zaman kanta mai rajin kare hakkin mutane masu manyan shekaru mai suna ‘Coalition of Societies for the Rights of the Older Persons in Nigeria’ (COSROPIN) ranar Talata a Abuja.
Hajiya Sadiya ta tabbatarwa da membobin kungiyar cewa ma’aikatar ta ta na kan aikin ganin an kafa cibiyar kuma ta fara aiki gadan-gadan.
Ta ce, “Yanzu haka akwai dokar da ta bada damar kafa cibiyar. Idan ta fara aiki, daga cikin ayyukan cibiyar akwai gano bukatun dattijai da damarmaki da ba su horo tare da fito da shirye-shirye don sama masu ababen more rayuwa da na wasanni, ilimi, kiwon lafiya da shakatawa don samun cikakken jin dadin rayuwa.”

Shugaban kungiyar ta COSROPIN, Sanata Eze Ajoku, ya gode wa ministar saboda kayan tallafin annobar korona (Cobid 19) wadanda ma’aikatar ta ba kungiyar don rage radadin wahalhalun da annobar ta jawo.

Ya yi wa ministar bayanai kan ayyukan kungiyar wadanda su ka hada da bin bahasin Tsarin Gwamnati kan Yawan Shekaru, da bibiyar neman tara kudin gudunmawa don inshorar kiwon lafiyar dattijai, da lissafa mutane masu yawan shekaru da kuma samar da dokar kula da dattijai, wato ‘Older Persons Rights and Pribilege Bill’.
Ajoku ya kuma bayyana cewa yunkurin samar da dokar kare hakkin dattijan mai suna ‘Older Persons Rights and Pribilege Bill’ har ya wuce karantawa na biyu a zauren Majalisar Dattawa, kuma ya na so ministar ta mara wa yunkurin baya.

Minista Sadiya ta shaida wa kungiyar cewa za ta goya mata baya, sannan ta kara da cewa dattijai na daga cikin gajiyayyu wadanda ma’aikatar ta damu da su.
Ta kara da cewa yawancin su sun bauta wa kasar nan a lokacin kuruciyar su, kuma har yanzu akwai dimbin gudunmawar da za su iya bayarwa saboda masaniyar su.
Ta ce saboda haka ne ma’aikatar za ta bada muhimmancin da ya kamata ga abubuwan da su ka shafe su a yayin da za ta tabbatar da cewa an rika tuntuɓar su a wajen aikin kafa cibiyar ta ‘National Senior Citizens Centre’.

Labarai Makamanta