Gwamnatin Tarayya Za Ta Karɓo Gagarumin Bashi – Ministar Kuɗi

Gwamnatin tarayya ta ce tana shirye-shiryen ciwo bashin Dala miliyan 750 daga bankin duniya don farfado da tattalin arzikin jihohin Nijeriya.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wajen bikin kaddamar da kwamitin farfado da tattalin arziki bayan barnar annobar korona (N-CARES) a Abuja ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba.

A cewar ministar, gwamnatin Nijeriya “tana kokarin ciwo bashin dala miliyan 750 a madadin jihohin, don farfado da tattalin arzikinsu da kuma tallafawa marasa karfi.

Dangane da tsadar rayuwa da kuma tasirin COVID-19 a Najeriya, ministar tace, za a garari matukar gwamnati tayi bata dauki mataki akan hauhawar farashi a Najeriya ba.

Jama’ar Najeriya na cigaba da ƙorafe-ƙorafe akan batun amso bashin da gwamnatin Buhari ke faman yi a Najeriya ba, inda wasu ke ganin rashin dacewar ciwo waɗannan basussuka da gwamnatin tarayya ke yi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply