Gwamnatin Tarayya Ta Yi Rawar Gani Wajen Bunkasa Fannin Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta himmatu sosai wajen ganin an samu ƙarancin yara waɗanda ba su zuwa makaranta a Najeriya.

Wannan magana ta na ƙunshe ne ciki wata sanarwar da Mai Bada Shawara Kan Inganta Rayuwa Marasa Galihu, Maryam Uwais.

An fitar da sanarwar ta hannun hadimar Uwais ɗin a fannin yaɗa labarai, Justice Bibiye.

Uwais ta yi bayanin ne a wurin taron bayar da horo na makonni uku ga matasan da suka kammala digiri su 500 a Gombe.

Matasan dai an koya masu horo ne a ƙarƙashin Shirin ARC-P, inda su ma idan su ka koma gida za su tashi tsaye wajen ƙoƙarin ganin an bunƙasa ƙarin yara zuwa makarantu.

Cikin shekarar 2018, wani bincike da UNICEF ta gudanar ya nuna Najeriya ce ɗaya a duniya wajen yawan yaran da ba su zuwa firare.

An bayar da adadin su zai kai yara miliyan 12.

Jihar Kano Ta Fi Kowace Jiha Yawan Yaran Ka Ba Bu Zuwa Makarantar Firamare -NBS/UBEC:

Wani binciken 2020 da Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar kwanan nan, ya bayyana yawan adadin ƙananan yara masu gararamba kan titina, ba su zuwa makarantun firamare a kowace jihar ƙasar nan.

Ƙididdigar wadda Hukumar Bayar da Ilmi a Matakin Farko (UBEC) ta taɓa fitar da irin sa a cikin 2018, ya nuna cewa a Jihar Kano akwai yara ƙanana masu gararamba kan titina har 989, 234.

Jihar Akwa Ibom ce ke bin Kano da yawan yaran da ba su zuwa makaranta, har yaro 581,800.

Sai kuma jihar Katsina, wadda ke da yara har 536,122.

Jihar Kaduna ta zo ta huɗu da yawan yara ƙanana waɗanda ke gararamba kan titina, har 524,670.

Ta biyar ita ce Jihar Taraba mai yara har 499,923.

Ita kuwa Jihar Sokoto, akwai yara 436,570 masu gararamba a kan titina.

Sai Jihar Yobe mai ƙananan yara da ba su zuwa makaranta har 427,230.

Jihar Zamfara kuwa akwai yara har 422,214. Sai ta goma ita ce Jihar Bauchi mai tulin ƙananan yara waɗanda ba su zuwa firamare har yaro 354,373.

Ƙididdiga ta kuma nuna cewa ƙasashen da ke da ƙarancin yaran da ba su zuwa makarantun firamare sun haɗa da Kuros Riba mai yara 97,919.

Sai Abia mai yara 91,548. Sai kuma Kwara yaro 84,247. Daga nan sai Enugu da ke da yara 82,051.

Jihar Bayelsa akwai yara 53,079 sai FCT Abuja mai yara 52,973. Yayin da Ekiti akwai yara 50,945.

Wannan ƙididdiga ta nuna jihar Kano da sauran jihohi 10 su ke da rabin yaran da ba su zuwa makaranta har miliyan 5.2 daga cikin yara miliyan 10.2.

Haka kuma ƙididdiga ta nuna yara miliyan 10.2 ne ba su zuwa makaranta, daga cikin yara miliyan 40.8 da ya kamata a ce su na makarantar firamare.

A jihar Yobe yara 427,230 ne daga cikin yara 983,469 ba su zuwa makaranta.

A jihar Sokoto mai yara miliyan 1,170,040, akwai yara 436,570 waɗanda ba su zuwa makaranta.

A jihar Ribas mai yara 554,927, akwai yara 188,590 waɗanda ke gararamba a kan titi, ba su zuwa makaranta.

Labarai Makamanta