Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 104 Domin Sayen Jannareta

Mafarkin samun wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya na kokarin gushewa kafin zuwan shekarar 2022 duba da yadda gwamnatin Buhari ta ware makudan kudi saboda saye da tattala janareta.

Wannan ya biyo bayan matakin da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya suka shigar na kashe kimanin Naira biliyan 104 wajen sayen janareto, man fetur da yi musu hidima a shekarar 2022.

Cikakkun bayanai na kunshe ne a cikin kudirin kasafin kudin shekarar 2022 wanda har yanzu majalisar dokokin kasar ba ta gama amince da shi ba.

Gwamnatin Buhari ta ware miliyoyin kudi domin aikin wutan Mambilla a shekarar 2022 Gwamnatin tarayya ta yi kasafin Naira miliyan 650 a matsayin kasonta na kwangilar wutar lantarkin Mambilla a shekarar 2022 mai zuwa.

A tsarin yarjejeniyar aikin wutan Mambilla, gwamnatin tarayya da kasar Sin za su yi karo-karo domin ayi wannan aiki da ake lissafi zai ci Dala biliyan 5.

Labarai Makamanta