Gwamnatin Tarayya Ta Shigar Da Sabbin Tuhume-Tuhume Kan Nnamdi Kanu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta sake shigar da kara kan tuhume-tuhume bakwai da ta yi wa gyara kan Nnamdi Kanu, shugaban haramtaciyyar kungiyar msu neman kafa Biyafra, IPOB da ke tsare.

Ƙarar da aka yi wa kwaskwarima mai lamba FHC/ABJ/CR/383/2015, wanda aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja na dauke da tuhume-tuhumen da a baya kotun ta amince da su.

Nnamdi Kanu, wanda a halin yanzu ya ke tsare hannun DSS, a yayin da ya ke mamba na haramtaciyyar kungiya, ya yi barazana ga rayuwur duk wani wanda ya saba dokar ‘zaman gida dole’ a kudu maso gabashin kasar a sakon da ya wallafa yana mai cewa duk wanda ya saba dokar ya rubuta wasiyyarsa.

Gwamnatin tarayya ta kara da cewa shugaban na IPOB da ranaku daban-daban daga 2018 zuwa 2021, ya yi jawabi kuma an ji a Najeriya, yana harzuka mutane su yi farautan jami’an tsaron Najeriya su kashe su da iyalansu, wanda hakan laifi ne karkashin sashi na 1 (2) (h) na dokar kare ta’addanci na 2013.

Labarai Makamanta