Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Fara Zirga-Zirgar Jirgin Abuja-Kaduna Yau Litinin

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna ba zai ci gaba da aiki ranar Litinin ba kamar yadda wasu kafofin yaɗa labarai suka ruwaito tun farko.

Wata majiya a Ma’aikatar Zirga-Zirgar Jiragen Ƙasa ta shaida wa BBC Hausa cewa sai “nan gaba kaɗan” jirgin zai dawo aiki kamar yadda ministan ma’aikatar ya sanar a baya.

A ranar Lahadi ne Minista Muazu Jaji Sambo ya kai ziyarar ganin gyaran da aka gudanar a kan titin jirgin sakamakon lalata shi da ‘yan bindiga suka yi a harin da suka kai a watan Maris wanda ya jawo dakatar da zirga-zirgar.

Jirgin ya yi tafiyar gwaji daga Abuja zuwa Kaduna a yau ɗin cikin shirye-shiryen da ake yi don komawarsa aiki.

Labarai Makamanta