Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Biliyan 173 Domin Daidaita Farashin Fetur

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa wasu bayanai da suka fito daga ma’aikatar albarkatun man fetur ta ƙasa ta ce gwamnatin tarayya ta bayar da kusan nairan biliyan 173.2 domin daidaita farashin sama da lita biliyan 11.6 na man fetur tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022 a faɗin ƙasar.

Gwamnatin Buhari ta biya kuɗin daidaita farashin man ne ta hanyar hukumar da ke kula da hada-hadar kasuwancin man fetur ta ƙasar.

Inda hukumar ƙayyade farashin man fetur ta NMDPRA ke tabbatar da daidata farashin man ta hanyar biyan kuɗin dakon man a manyan motoci zuwa gidajen mai a faɗin ƙasar.

To sai dai duk da waɗannan biliyoyin kuɗaɗe da hukumar ke cewa ta biya, domin daidai farashin, har yanzu ana sayar da man a mabambantan farashi a fadin ƙasar.

Labarai Makamanta