Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Bashin Kudin ‘Yan Fansho Tiriliyan 8.29 Dake Banki

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta karbi bashin kuɗi har Naira Trilliyan 8.29cikin kudin yan fansho Naira Trilliyan 12.9 dake ajiye a babban Bankin kasa.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa duk da rashin amincewan da mutane suka nuna bisa wannan niyya a baya, gwamnati ta bi ta bayan fagge da sunan zuba jari wajen karban kudaden.

Idan jama’a ba su manta ba shekarar 2019, majalisar tattalin arzikin Najeriya ta bukaci karban bashin N2 trillion daga kudin fansho don yi wasu manyan ayyuka a fadin Najeriya, amma ‘yan Najeriya suka bayyana cewa sam hakan ba zai yiwu ba.

A baya mun kawo muku cewa, gwamnatin tarayya na shirin aron kudaden yan Najeriyan da ke asusun da aka dade ba’a waiwayesu ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba’a bibiya ba.

Gwamnatin zata samu daman yin hakan ne bisa dokar kudin 2020 da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu. Karkashin sashe na 12 na dokar, an bayyana cewa za’a iya aron kudaden masu hannun jarin da ajiya na mutanen wanda suka kai shekaru 6 ba’a waiwaya ba. Gwamnati tace duk kudaden da ba’a bibiya ba za’a aika su wani asusun lamuni na musamman mai suna ‘Unclaimed Funds Trust Fund’.

Labarai Makamanta