Gwamnatin Tarayya Ta Fara Raba Wa Talakawa Kudade A Jigawa

Rahotanni daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta dawo rabon kudi N5,000 na shirin CCT na ma’aikatar jinkai da walwalan jama’a ga al’ummar Jihar Jigawa ranar Juma’a, 20 ga Nuwamba, 2021.

An ruwaito cewa jama’a sun yi gangami a wuraren bada kudi a karamar hukumar Kiyawa ta jihar. A cewar rijistan rabon kudin, sama da talakawa mutum 167,620 ake sa ran zasu samu rabonsu cikin N1.6 billion.

Rahoton ya kara da cewa mutane sun tafi wajen da katunansu domin karban kudi.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da kudin, Hajara Rabi’u ta bayyanawa manema labarai farin cikinta game da wannan kudi.

Labarai Makamanta