Gwamnatin Tarayya Ta Fara Raba Tallafin Korona A Arewa Maso Gabas

Gwamnatin tarayya ta fara raba tallafin kudi ga talakawa da gajiyayyun mata wadanda rikicin Boko Haram da annobar korona ya ritsa da su a Shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

Ministar ma’aikatar jin ƙai da walwala ta Gwamnatin tarayya Hajiya Sadiya Farouk, a yayin ƙaddamar da shirin a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, tace burin tallafin shine samar da wadataccen jari ga matan domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Sadiya Faruq ta ƙara da cewa gwamnatin jihar Yobe ta amshi kudi fiye da Naira Miliyan 980 karkashin shirin gwamnatin tarayya na raba kudade tun daga fara shi.

Kimanin kananan hukumomi 6 ne ke cin gajiyar shirin a jihar ta Yobe, kuma shirin zai faɗaɗa ya game dukkanin ƙananan hukumomin Jihar ya ketara sauran Jihohin dake Shiyyar gaba ɗaya.

Minista Sadiya ta yi bayanin cewa za’a raba dubu 20 ga kimanin mutane dubu 10 domin rage raɗaɗin annobar cutar korona. An kirkiro shirin tallafin kudin ne a karkashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari domin rage raɗaɗin talauci.

Labarai Makamanta