Gwamnatin tarayya ta sanar da dawo da darasin tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a cikin manhajar ilimi na matakin farko a Nijeriya, shekaru 13 bayan an soke shi.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a Abuja, wajen bikin kaddamar da shirin sake koyar da ilimin tarihi da horar da malaman tarihi a matakin farko.
Ya nuna damuwar sa da yadda hadin kai a Nijeriya ya yi ƙaranci, inda mutane su ka saka kabilanci a zuƙatansu, inda ya ƙara da cewa rashin samun ilimin yadda Nijeriya ta kafu, sakamakon soke darasin tarihi a makarantu da a ka yi a manhaja.
Ya ce an fitar da jimillar malaman tarihi guda 3,700 domin horas da su a zagayen farko na koyar da darasin.
You must log in to post a comment.