Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin Janye Tallafin Mai

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar Harkokin kudi Zainab Ahmed ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta janye shawarar da ta dauka a baya na cire tallafin mai a cikin wannan shekara.

Minista ta ce ganin yadda rayuwa yayi tsanani ba zai yiwu a ce za a cire tallafin man domin talakawa zasu dada fadawa cikin gungurmin talauci ne wanda dama suna fama ne da ita.

A dalilin haka gwamnati ta wancakalar da waccan shawarar, ba za ta cire tallafin mai a watan Yuli ba kamar yadda ta fadi a shekarar bara.

Minista zainab ta ce bangaren zartaswa za ta aika wa majalisar Kasa da sabon kudirin karin kudi a kasafin kudin 2022 domin cike gurbin gibin da za a samu domin biyan kudin tallafin wanda babu shi a kasafin da Buhari ya saka wa hannu.

Dama kuma idan ba a manta ba kungiyoyin kwadago da nan ma’aikatun mai kaf din su sun ce da zarar gwamnati ta kafe a matsayinta na cire tallafin za a shiga yajin aikin gama gari sai baba ta kira.

Haka shima shugaban majalisar Dattajai, Ahmed Lawal wanda dashi aka yi zaman yace ba zai yiwu gwamnati ta cire tallafi yanzu ba a halin da talakawa ke ciki a kasar nan.

Ya yi kira ga kungiyoyin da su yi hakuri su janye shirin afkawa yajin aikin.

Labarai Makamanta