Gwamnatin Tarayya Ta Buƙaci Jihohi Su Dakatar Da Yin Rigakafin Korona

Gwamnatin Nijeriya ta umarci jihohi 36 da babban birnin tarayya da su gaggauta dakatar da yi wa al’umma Rigakafin cutar Corona, ta farko ta AstraZeneca da zarar sun yi amfani da rabi daga cikin kasonsu da aka raba masu domin samun damar bayar da rigakafin ta biyu ga wadanda aka yi wa ta farko.

Ministan lafiya Osagie Ehanire wanda ya bayar da umurnin ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da tabbas kan lokacin da za ta samu karin rigakafin bayan Indiya ta dakatar da fitar da dukkanin rigakafin da cibiyar Serum a kasar ke samarwa.

“Mun yi tunanin cewa ya fi dacewa a kammala yi wa waɗanda aka fara yi wa rigakafin gaba ɗaya,” in ji ministan.

A ranar 2 ga watan Maris ne Najeriya ta karɓi rigakafin korona kusan miliyan 4 na AstraZeneca.

Labarai Makamanta