Gwamnatin Oyo Ta Koka Akan Tsadar Kayan Masarufi A Jihar

Gwamnatin Jahar Oyo ta fitar da wata muhimmiyar sanarwa a jiya juma’a, duba ga yanda kayan masarufi yayi tashin gwauron zabi a duk fadin jahar Nata.”

“A halin yanzu dai abubuwa sai Dada ta6ar6arewa suke a jahar ta Oyo, sakamakon karancin kayan Abinci, dake addabar jahar.

“A nan kuma gefe kungiyar dillalan kayan Abinci dake arewacin Najeriya, sun lashi takobin kauracema kai kayan Abinci zuwa kudancin kasar nan, bama jahar Oyo kadaiba, duba ga yanda ake cin zarafin ‘yan uwansu hausawa, tare da sauran mazauna Garin dake kudancin kasar nan.

Gwamnatin ta kuma kara da cewa koba komai akwai hausawa dake zaune a jahar, kuma harda su wannan tsadar kayan masarufin ke shafa.”

La’akari da karancin kayan na abinci da yayi shura, gwamnatin jahar Oyo, tana kira ga dillalan kayan Abinci dake Arewacin Najeriya, dasu janye wannan manufar tasu da babu gaira babu dalili a cewar gwamnatin ta Jahar Oyo a takardan manema labarai.

Shin ko masu karatu kun goyi bayan cigaba da dakile hanyoyin kaiwa “yan kudancin kasar nan kayan Abinci daga nan arewacin kasar nan ?

Labarai Makamanta