Gwamnatin Kaduna Ta Tsawaita Haramcin Hawa Babura

Gwamnatin jihar Kaduna ta kara wa’adin hana amfani da mashin, wanda aka fi sani da ‘Okada’ ga yan kasuwa da kuma ɗai-ɗaikun mutane har sai baba ta gani.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin Gida, Samuel Aruwan, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Talata.

Kwamishinan yace hana Okada da sauran matakan da gwamnatin jihar Kaduna ta ɗauka na nan daram.
“Gwamnatin Kaduna na sanar da al’umma cewa hana amfani da mashin, wato Okada, yana nan daram har sai baba ta gani.”

Sauran matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka, wanda a cewar Aruwan za su cigaba da kasancewa har sai an ji daga gwamnati, sune kamar haka:

-Hana yawo da makamai masu hatsari.

-Hana amfani da mashin mai kafa uku wanda aka fi sani da Keke Napep da daddare.

Labarai Makamanta