Gwamnatin Kaduna Ta Karyata Sace Ɗaliban Firamare

A wajen wani taron manema labarai da ya gudana a Kaduna Kwamishinan tsaro na Jihar Samuel Aruwan, ya bayyana cewar bayan samun sanarwar da suka yi da safiyar ranar Litinin game da daliban Firamare a Birnin Gwari, a halin da ake ciki tuni Gwamnatin ta kammala tattara bayanai kuma ta samu labarin bacewar malamai Uku na Firamaren Rema da ke yankin mazabar Magajin Gari

Malaman makarantar da aka kama sun hada da Rabiu Salisu, Umar Hassan da Bala Adamu. Kuma bayanan sun tabbatar da cewa babu wani yaro dalibi cikin ‘yan makarantar Firamaren da aka kama.

Sai dai kawai daliban da suka halarci makarantar sun samu kansu cikin wani hargitsi ne sakamakon harin da maharan suka kai a kan Babura, yanayin da aka shiga a makarantar ya yi sanadiyyar rashin samun dalibai guda biyu da suka hada daAhmad Halilu da Kabiru Yahaya, amma a halin yanzu duk an gansu cikin koshin lafiya da walwala.

 Rahotannin tsaro da Gwamnati ta samu sun bayyana mata cewa wadansu mahara sun sace shanu,Babura biyar da sauran kayayyaki da dama.

 Kwamishinan ya ci gaba da bayanin cewa wadansu sojojin Nijeriya da ke aikin sintiri a cikin Dajin kananan hukumomin  Kachiya da Kauru sun yi nasarar tsintar wata yarinya mai suna Fatima Lawal da ta kubuta daga yan bindiga. Kuma kamar yadda bayaninta ya nuna cewa an sace ta ne sati uku da suka gabata a wani kauye mai suna Randa, a yankin Kadage, karamar hukumar Kauru duk cikin Jihar Kaduna.

 Kuma tuni aka mika wadannan yara a hannun iyalansu ta hannun shugabannin kananan hukumomin Chikun da Kauru.

Sai kuma wadansu jami’an sojan da ke aikin sintiri a Faka da ke karamar hukumar Chikun sun tsinci wani saurayi mai shekaru 14 da ke gararamba a cikin dajin Faka da ya bayyana masu cewa sunansa Adewale Rasaq, da aka sace sama da sati daya a unguwar Kudenden a karamar hukumar Chikun, wanda ya ce ana ta dai-daitawa da iyayensa kan a biya kudi naira miliyan 15 amma ya samu kubuta daga yan bindigar.

A kokarin Gwamnati na ganin ta kakkabe yan Ta’adda tare da ayyukansu a Jihar baki daya ta samar da lambobin wayar ta fi da gidanka ta duk wanda ke da wani bayanin da zai amfanar a samu nasarar samun ingantaccen tsaro.Ga dai lambobin kamar haka 09034000060,08170189999.

Labarai Makamanta