Gwamnatin Buhari Kyanwar Lami Ce – Sardauna


An bayyana Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Buhari, a matsayin Gwamnatin mara karsashi wadda ta samu nakasu da kuma tawaya a wajen sauke nauyin dake rataye a kafaɗunta.

Alhaji Hassan Sardauna ɗan siyasa kuma mai sharhi akan al’amuran yau da kullum ya kwatan ta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da kyanwar lami wanda bata cizo balle yakushi, kuma hakan na daya daga cikin dalilan dake sa kowa ke abinda yaga dama a gwamnatin.

Hassan Sardauna ya bayyana hakan ne a cikin shirin babbar magana da ake gabatarwa duk ranar lahadi a gidan talbijin da rediyo na liberty dake babban birnin tarayya abuja.

Yace idan ka dubi maganar da mai ba shugaban kasa shawara akan tsaro janar Babagana Mungonu yayi akan batar makudan kudaden tsaro da kuma yadda ya dawo ya sauya kalaman nasa kasa da awanni 24 kacal ya isa mai tunani da hangen nesa yasan akwai babbar matsala kuma wasu daga cikin matsalolin sai a karshen mulkin Buhari za a gano su kamar yadda akai a mulkin Jonathan.

Kuma inda ace shugaban kasa yana yaki da rashawa kamar yadda aka sanshi a baya ne da yanzu anfara binciken abinda ya faru sannan inda a sauran kasashen duniya ne da janar mungonu ya ajiye aikin sa domin bayyana hakan da yayi ya nuna kamar baisan aikin sa ba.

Sannan maganar Buratai yace bai ci ko sisin kwabo ba baima taso ba, domin dole sai ya jira kwamitin bincike tayi binciken ta ta fitar da rahoto kamin asan hakikanin gaskiyar sa akan lamarin.

Sannan maganar cewar wata ma’aikatar kayyade farashin mai ta wayi gari tace an kara kudin mai zuwa naira 212, sannan gwamnatin tarayya ta fito ta karyata, kuma har wasu gidajen mai su fara saida man a haka ko kuma su kulle gidajen man su wahalar da yan najeriya wurin Neman man fetur.

Dukansu babu wanda gwamnatin ta hukunta har zuwa yanzu, wannan kadai ya isheka sanin cewar gwamnatin Buhari ta zama kyanwar lami wadda bata cizo balle yakushi. ”Inji Hassan Sardauna

Labarai Makamanta