Gwamnatin Buhari Ba Ta San Darajar Talaka Ba – Aisha Yesufu

Sananniyar matar nan mai rajin fafutukar dawo da ‘yan matan Chibok Aisha Yesufu ta koka a kan kunnen uwar shegu da gwamnatin tarayya tayi da lamarin ‘yan makarantar tsawon shekaru masu yawa.

Aisha ta ce da zaran ranar 14 ga watan Afrilu yayi, sai gwamnati ta fito tayi jawabi kan yaran, inda a cewarta daga nan sai tayi watsi da lamarin sai kuma wata shekara.

A hira da manema labarai suka yi da ita, mai fafutukar ta ce ya kamata gwamnati ta dunga tattaunawa da iyayen yaran don basu baki amma bata yin haka, kuma babu alamar zata yi hakan.

Ta ci gaba da cewa babu wani taimako da gwamnati ke yi wa iyayen koda kuwa ta maganar fatan baki ne. Hakan kuma rainin hankali ne.

Game da ko akwai wani taimako da gwamnati ke baiwa iyayen yaran, Aisha Yesufu ta ce: “Babu abunda gwamnati ke yi masu ko waya ko a hada su a basu jawabi. Sai dai ma iyayen sukan kira mu lokaci zuwa lokaci suna tambayanmu shin don Allah mun ji wani abu ko an fada mana wani abu mune ke Abuja.

“Abin da bakin ciki da rainin hankali, babban abin da yake za ka ga gwamnatin Najeriya idan mutane suka ga talakawa irin rainin da suke yi wa talakawa ba kadan bane, amma idan lokacin da za a yi zabe ne sun san cewa talakawa ne ke fitowa zabensu suke sa su a wajen.

Amma idan lokacin da za a basu shugabanci nagari ne sai a dunga yi masu rashin mutunci. “Na tabbata da yaran Chibok yaran masu kudi ne da babu wanda zai yi masu wannan rashin mutuncin ko magana mai dadi babu.

Labarai Makamanta