Gwamnati Mai Ci Ta Jefa ‘Yan Bauchi Cikin Talauci – Sadiq Baba Abubakar

Daga Adamu Shehu Bauchi

Tsohon Shugaban Sojin sama kuma dan takrar kujerar gwamna karkashin jamiyyar APC a jihar Bauchi Sadique Baba Abubakar yace gwamnatin jihar tayi watsi da hidimar moma inda yace hakan ya jefa dumbin manoma ciki rashin tabbas da talauchi,

Kana yayi alkawarin farfado da tattalin arzikin jihar ta fannin noma a dukkan fadin jihar in aka bashi dama a zaben 2023.

Yayi wan nan Kalaman ne, a karamar hukumar Misau lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a dakin taro na Musamman don ganin sun mara mashi baya a zaben dake tafe a watan uku cikin wan nan watan

“yace gwamnatin jiha ta gagara lalubu mafita ta hanyar cire miliyoyin alummar jihar Bauchi cikin kangin yunwa da halin kaka nikayi da rashin aikin yi ga matasa da mata,

yace yau a jihar Bauchi talaka baya iya cin abinci sau uku a gidansa, a cewarsa talauchi yana kara ta’azzara a fadin jihar, don haka gwamntinmu zata tashi tsaye ta gyra wan nan matsala”

Tun a farko dan takarar ya zauna da yan’kasuwa a karamar hukumar inda yayi masu alkawarin samar da hanyoyin raya kasuwanchinsu

Tsohon sojan yana ci gaba da jan hankalin alumman jihar a lokacin gangamin kampe dasu yadda da manufofinsa su zabe shi a matsayin gwamna jihar don chanji mai dorewa da walwala a cikin rayuwar takala.

Labarai Makamanta